Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ta amsa tambayoyi a FBI

‘Yan takarar shugabancin Amurka a Jam’iyyar Democrat Hillary Clinton ta amsa tambayoyi daga Hukumar bincike ta FBI kan yadda ta yi amfani da kafar sadarwa ta email mallakinta a lokacin da tana sakatariyar harakokin wajen kasar.

Hillary Clinton ta Democrat
Hillary Clinton ta Democrat EUTERS/Rick Wilking
Talla

Wani da kusa da ita ya ce an shafe sa’o’I uku da rabi Clinton na amsa tambayoyi a shalkwatar hukumar FBI a Washington.

Wannan na zuwa ne a yayin da ya rage makwanni uku kafin babban taron jam’iyyar Democrat da za a tsayar da ita ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar da ke mulki a Amurka.

Binciken da ake akan Clinton na iya haifar da Baraka idan har masu kada kuri’a suka fara shakku kan aikata rashin gaskiya akan zargin da ake ma ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.