Isa ga babban shafi
Amurka

Trump da Hillary sun yi mamaya

Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat na ci gaba da mamaye zaben fidda gwanin da ake yi a Amurka, bayan samun nasara a zaben da aka gudanar a jihohi biyar a jiya Talata.

'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton.
'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton. REUTERS/Mike Segar
Talla

Sakamakon zaben dai gagarumar nasara ce ga ‘Yan takarar biyu da ke neman shugabancin Amurka.

Trump ya sake doke Ted Cruz da John Kasich a a zaben Talata da aka gudanar a Jihohin Connecticut da Delaware da Maryland da Pennsylvania da Rhode Island.
Clinton ta lashe Jihohi 4 daga cikin 5, abokin hammayarta Bernie Sanders ne ya lashe zaben a Jihar Rhode Island.

Wakilin RFI Hausa a Amurka, Yakubu Lukman y ace yanzu zai yi wahala ga sauran ‘Yan takarar su cim ma Trump da kuma Clinton a zabukan na fitar da gwani.

Bayan samun nasara, Donald Trump ya mika godiyarsa ga jama’ar shi.

A nata bangaren Hillary Clinton tace za ta yi kokarin hada kan jam'iyyar Democrat domin samun nasara zaben shugaban kasa, tare da kirkiro sabuwar Amurka da kowa zai samu ci gaba.

Clinton ta ce za ta samar da Amurka da za a girmama juna, maimakon kaskantar da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.