Isa ga babban shafi
Amurka

Hillary da Trump sun samu nasara a New York

Hillary Clinton ta Jam’iyyar Democrat da Donald Trump na Republican sun samu gagarumar nasara a zaben fitar da gwanin takarar shugabancin Amurka da aka gudanar a ranar Talata a New York na Amurka.

Donald Trump  na Republican da Hillary Clinton ta Democrat
Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat PHOTO DESK / AFP
Talla

Clinton ta samu kashi 57 a Jam’iyyar Democrat fiye da Bernie Sanders, yayin da Trump ya samu kashi 60 a Jam’iyyar Republican fiye da babban mai hammaya da shi Ted Cruz.

Wannan dai ya karawa ‘Yan takarar biyu kwarin guiwar zama ‘Yan takarar shugabancin Amurka a zaben Watan Nuwamba.

Yanzu ya rage ga ‘Yan takarar su samu nasara a Jihohin Connecticut da Delaware da Maryland da Pennsylvania da Rhode Island a zaben fitar da gwanin da za a gudanar a ranar 26 ga watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.