Isa ga babban shafi
Amurka

Zaben Amurka: Sanders ya doke Clinton a Jihohin Alaska da Washington

Dan takarar shugabanci Amurka a Jam’iyyar Demokrat Bernie Sanders ya lashe zaben fidda gwani a Jihohin Alaska da Washington da gagarumin rinjaye inda ya doke Hillary Clinton.

'Yan takarkarin Demokrat Hillary Clinton da Bernie Sanders
'Yan takarkarin Demokrat Hillary Clinton da Bernie Sanders REUTERS/Jim Young
Talla

Nasaran Sanders ba karamin cikas ya haifar ga abokiyar takararsa Clinton ba, dake kan gaba da yawan kuri’u a zaben Fidda gwamni da ake cigaba da gudanawar a Amurka domin tsayar da dan takarar Jam’iyya.

Sanders ya doke Clionton ne da kashi 79.2 cikin 100 yayin da ita ke da kashi 20.8 cikin 100 a Alaska, a Washinton kuma yana da kashi 72.1 cikin 100, ita kuma ta samu Kashi 27.

A cewar Sanders da a yanzu ke da yawan kuri’u 952 yayin da Clinton ke da 1,711 ya ce Nasaran Alaska da Washington ya kara masa kwarin guiwa a cigaba da fafatawar su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.