Isa ga babban shafi
Amurka

Cruz da Sanders sun samu nasara a Wisconsin

Sanata Ted Cruz da Bernie Sanders sun lashe zaben fitar da gwani da aka yi a Jihar Winconsin, abin da ke zama koma baya ga Donald Trump da Hillary Clinton.

Senatan Texas Ted Cruz ya lashe zaben fitar da gwani a Wisconsin
Senatan Texas Ted Cruz ya lashe zaben fitar da gwani a Wisconsin REUTERS/Kamil Krzaczynski
Talla

Nasarar Ted Cruz kan Donald Trump wani alamu ne ne da ke nuna cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da fafutukar samun tikitin takarar Jam’iyyar.

Bernie Sanders na Jam’iyyar Democrat ya samu kashi 55 na kuri’un da aka kada sabanin 44 da Hillary Clinton ta samu.

Zuwa yanzu dai an gudanar da zaben fitar da gwanin a jihohi 36, kuma Hillary Clinton ta lashe Jihohi 20, yayin da abokin hammayarta Bernie Sanders ya lashe Jihohi 16.

Jihohi 34 aka gudanar da zaben a bangaren Jam’iyyar Republican, kuma Donalt Trump ya lashe jihohi 20m yayin da Ted Crus ya samu nasara a Jihohi 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.