Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ta samu yawan Wakilai don zama ‘Yar Takara

Rahotanni daga kasar Amurka sun ce Hillary Clinton ta samu yawan wakilan da ake bukata dan zama Yar takarar shugabancin kasar a Jam’iyyar Democrat tun kafin zaben fitar da gwani da za a gudanar a yau Talata a Jihohi 6.

'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton.
'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton. REUTERS/Dominick Reuter
Talla

Kafofin yada labaran Amurka sun ce Clinton ta samu yawan wakilan da suka zarce 2,383 da ake bukata don samun tikitin Jam’iyyar.

Wannan nasarar za ta ba Hillary Clinton damar zama shugabar kasa mace ta farko a Amurka idan har ta doke dan takarar Jam’iyyar Republican a zaben watan Nuwamba.

Zaben fitar da gwanin na yau Talata shi ne na karshe wanda za a gudanar a jihohin California mai yawan masu jefa kuri’a da kuma New Jersey.

Kuma sakamakon zaben zai tabbatarwa Hillary Clinton zama ‘yan takara idan har ta samu nasara a California Jiha mafi girma a Amurka.

Hillary dai ta dada samun gwarin guiwa sakamakon Nasarar da ta samu a zaben da aka gudanar a Puerto Rico da Virgin Island fiye da abokin takararta Bernie Sanders.

Cllinton tace idan har ta samu nasara a yau, abu na farko da za ta sa gaba shi ne hada kan ‘ya’yan jam’iyyar Democrat.

Tuni da Clinton ta shirya gagarumin biki a New York amma Sanders na ci gaba da yakin ganin ya samu nasara a California.
Ana sa ran shugaban Amurka Barack Obama zai sanar da marawa Clinton baya idan har ta samu nasara a zaben yau Talata.

Clinton dai na kan gaba da yawan kuri’u akan Sanders a zabukan fitar da gwanin da aka gudanar a jihohin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.