Isa ga babban shafi
Amurka

Democrat ta tabbatar da takarar Hillary Clinton

Hillary Clinton ta kafa tarihi a kasar Amurka sakamakon amincewa da ita a matsayin yar takarar shugabancin kasar a babban taron Jam’iyyar Democrat. 

Hillary Clinton a Taron Democrats na kasa a Philadelphia na Amurka
Hillary Clinton a Taron Democrats na kasa a Philadelphia na Amurka REUTERS/Brian Snyder
Talla

Wannan shine karo na farko da aka zabi mace tayi takara a wanann matakin.

Hillary, tsohuwar matar shugaban kasar Amurka da kuma sakataren harkokin waje ta kai ga wannan nasara ne bayan doke abokin hamayarta Bernie Sanders a zaben fidda gwani.

Jiga-jigan jam’iyyar Democrat sun bukaci a fito kwai da kwar-kwata domin jefa wa Hillary Kuri’u a zaben shugaban kasa da zasu fafata da Trumph na Republican a watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.