Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya bukaci a zabi Clinton a zaben Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga 'ya'yan jam’iyyar Democrat da su zabi Hillary Clinton don ganin ta kada Donald Trump a zaben shugabancin kasar, inda ya ke cewa babu gwaji tsakanin 'yan takaran biyu a zaben watan Nuwamba.

Shugaba Barack Obama da Hillaru Clinton a wajen babban taron jam'iyyar Democrat a Amurka
Shugaba Barack Obama da Hillaru Clinton a wajen babban taron jam'iyyar Democrat a Amurka AFP
Talla

A jawabin da ya yi wanda ya tada tsimin mahalarta baban taron Jam’iyar a Philadelphia, shugaba Obama ya jaddada matsayinsa na cewa, a halin da Amurka ke ciki a yau, babu wadda tafi dacewa ta shugabance ta kamar Hillary Clinton.

Wakilinmu daga Amurka Yakubu Lukhman na dauke da rahoto game da wannan batu.

01:36

Rahotan Yakubu Lukman kan taron Democrat

Shi ma mataimakin shugaban kasar ta Amurka, Joe Biden ya gabatar da nasa jawabin a babban taron, inda ya caccaki Donad Trump na Republican tare da bayyana shi a matsayiin mai goyon bayan azabtar da jama'a da kuma nuna kyama da wasu mabiya addini.

Mr. Biden ya ce, Trump ba shi da masiya kan da yadda Amurka ke samun daukaka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.