Isa ga babban shafi
Amurka

Za a yi magudi a zaben Amurka- Trump

Dan takarar Republican Donald Trump ya yi zargin cewa ana shirin yin magudi a Zaben shugaban kasa a Amurka bayan ya ce an yi wa Bernie Sanders magudi a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar Democrat.

Dan takarar Jam'iyyar Republican a zaben Amurka Donald Trump
Dan takarar Jam'iyyar Republican a zaben Amurka Donald Trump EUTERS/Carlo Allegri
Talla

Bernie Sanders dai ya yi takara da Hillary Clinton a zaben fitar da gwani na Democrat, kuma tuni ya bayyana nuna goyon bayan shi ga Clinton wacce aka tsayar a matsayin ‘Yar takarar Jam’iyyar.

Amma Trump ya soki Sanders game da Clinton inda ya ce ya marawa Shaidaniya baya.

A lokacin da ya ke jawabi a wani gangami a Columbus Jihar Ohio, Trump ya ce yana tsoron za a murde zaben shugaban kasa kamar yadda aka murde zaben fitar da gwani na Democrat.

Trump dai na ci gaba da fuskantar suka daga bangaren Jam’iyyarsa ta Republican inda manyan ‘Yan siyasa ke caccakarsa game da kalaman shi akan iyayen wani sojan Amurka musulmi da aka kashe a yakin Iraqi.

Sakamakon Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CNN ta gudanar ya nuna Clinton ta samu nasara da kashi 52 fiye da Trump da ya samu kashi 43.

Sakamakon ra’ayin Jama’a na kafar CBS ya nuna cewa cikin masu jefa kuri’a 6 a cikin 10 sun yi imanin Trump bai shirya zama shugaban kasa ba, yayin da kashi 60 suka ce Clinton ta fi cancanta

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.