Isa ga babban shafi
Amurka

''Za a yi shugaba mara kan gado a Amurka''

Wasu masana harkar tsaron kasa 50 daga Jam’iyyar Republican ta kasar Amurka sun bayyana Donald Trump, dan takarar Jam’iyyarsu a matsayin shugaban mara kan gado da kasar zata samu a tarihin Amurka, don haka ba zasu zabe shi ba.

Donald Trump, dan takarar shugabancin kasar Amurka karkashin jam'iyar Republican.
Donald Trump, dan takarar shugabancin kasar Amurka karkashin jam'iyar Republican. EUTERS/Carlo Allegri
Talla

Masanan 50 da suka hada da tsohon Daraktan hukumar leken asiri ko CIA Michael Hayden sun rubuta wasika dauke da sanya hannun su wanda ke nuna cewar Trump bashi da kwarewa da ladubba da kuma halaye na gari da zai jagoranci Amurka, inda kullum yake zubar mata da mutunci a idon duniya.

Wannan wasika na zuwa ne a dai dai lokacin da manyan yayan jam’iyyar Republican ke ci gaba da nesanta kansu daga dan takaran.

Sai dai a martanin da ya mayar, Donald Trump ya bayyana masana harkar tsaron a matsayin wadanda suka gurbata duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.