Isa ga babban shafi
Brazil

Rousseff na fuskantar tsigewa

Majalisar Kasar Brazil ta amince ta ci gaba da shirin ta na tsige shugabar kasar Dilma Rousseff wadda ake zargi da laifin almundahana a kasar. 

Shugabanr kasar Brazil Dilma Rousseff da aka dakatar
Shugabanr kasar Brazil Dilma Rousseff da aka dakatar REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Yan Majalisu 59 suka amince da bukatar yayin da 21 suka k,i bayan kwashe dogon lokaci ana tafka mahawara.

Wannan nasara zata baiwa Majalisar damar cigaba da shirin tuhumar shugabar daga ranar 25 ga watan nan, kwanaki 4 bayan kamala gasar Olympics.

Kafin fara mahawarar sai da shugaban kotun kolin kasar Ricardo Lewandoski ya shaidawa yan majalisu cewar suna sirin fara amfani da makami mafi tsauri da kundin tsarin mulki ya basu dama, saboda haka su sanya kishin kasa cikin ayyukan su.

Ana bukatar kuri’u 81 a Majalisar domin tsige Rousseff daga kujerar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.