Isa ga babban shafi
Brazil

Borin kifar da gwamnatin Dilma Rousseff a Brazil

Dubban Mutane ne suka kwarara titunan kasar Brazil a wani sabon yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Dilma Rousseff saboda zargin da ake mata na cin hanci da rashawa.

Borin tsige Dilma Rousseff a Brazil
Borin tsige Dilma Rousseff a Brazil REUTERS/Nacho Doce
Talla

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki bayan gurfanar da tsohon shugaban kasar Inacio Lula da Silva a gaban kotu saboda tuhumar da ake masa na halarta kudaden haramun.

Akalla mutane miliyan guda ne aka yi hasashen cewar sun shiga zanga zangar dan neman ganin an sauke shugaba Dilma Rousseff daga karagar mulki da kuma gurfanar da ita a gaban shari’a dan amsa tambayoyi kan rawar da ta taka a zargin da ake mata.

Ana dai tuhumar shugaba Rousseff ce da hannu cikin badakalar cin hanci a kanfanin man Brazil da ake kira Petrobraz, zargin da ya shafi akasarin jami’an tsohuwar gwamnatin shugaba Lula da dama.

A babban birnin kasar Brasilia, akalla mutane 20,000 suka halarci zanga zangar da safe, inda adadin ya tashi zuwa yamma.

A birnin Rio rahotanni sun nuna cewar masu zanga zangar sun titin Avenida Atlantica zuwa bakin tekun Copacabana.

Da yawa daga cikin masu zanga zangar sun sanya rigar kungiyar kwallon kafar kasar.

Shugaba Rousseff ta bukaci masu zanga zangar suyi ta cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.