A na tuhumar tsohon shugaban kasar Brazil
Masu gabatar da kara a Brazil sun shigar da kara inda su ke tuhumar tsohon shugaban kasar Inacio Lula da Silva da laifin halarta kudaden haram, a wani yunkuri da ake ganin na iya kifar da gwamnatin kasar da ya taimaka wajen dora ta kan karagar mulki.
Wallafawa ranar:
Ofishin mai gabatar da kara ya ce, tsohon shugaban da ya yi suna wajen farfado da tattalin arzikin Brazil da kuma sanya ta cikin kasashen da arzikinsu ke saurin habbaka, ya boye wani gidan alatu da ya mallaka a bakin tekun Sao Paolo da kuma wani a Guaruja wanda hakan babban laifi ne.
An dade ana zargin gwamnati mai ci ta shugaba Dilma Roussefff wadda tsohuwar babbar hafsa ce a ofishin Lula da cin hanci da kuma halarta kudaden haramun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu