Isa ga babban shafi
Brazil

Shirin tsige uwargida Dilma Roussef daga shugabancin Brazil

Shugaban Majalisar kasar Brazil Eduardo Cunha ya kaddamar da shirin tsige shugabar kasar Dilma Rousseff saboda zargin da ake mata na cin hanci da rashawa.

Uwargida  Dilma Rousseff Shugabar kasar Brazil
Uwargida Dilma Rousseff Shugabar kasar Brazil
Talla

Cunha yace bayan ya dade yana watsi da bukatar tsige shugabar kasar yanzu ya gamsu da sheidun da ya samu cewar shugaba Rousseff na da hannu wajen badakalar cin hanci da ya dabaibaye bangaren man fetur din kasar.

Wani kwamiti Majalisar na musamman ne zai duba bukatar shugaban Majalisar kafin amincewa ko a cigaba da shirin tsige shugabar ko kuma ayi watsi da shi.

Yanzu haka hukumar dake yaki da cin hanci ta kama fitatun yan kasuwa da yan siyasar kasar da dama saboda zargin da ake musu na hannu cikin cin hancin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.