Isa ga babban shafi
Brazil

Uwargida Dilma Roussef na tsaka mai wuya

A kasar Brazil karamar Majalisar Dokokin zata kada kuri'ar  amincewa ko rashin amincewa da tsige shugabar kasar  Dilma Rouseff, bayan gudanar da wata mahawara da aka dauki lokaci ana yi a yau juma’a.

Dilma Roussef Shugabar kasar Brazil
Dilma Roussef Shugabar kasar Brazil REUTERS/Adriano Machado
Talla

Bayan tafka doguwar mahawara kan batun tsige shugabar Brazil,yan Majalisun za su soma sabuwar mahara da zata kai su ga matakin kada kuri'a don amincewa da tsige shugaba Dilma Roussef.

Nan da karshen wannan makon mai kamawa ne ake sa ran za a kaɗa ƙuri'a tsakanin mambobin majalisar mai yawan mutane 513, bayan sakamakon zaben ne za’a a je ga batun tsige shugabar Uwargida Dilma Roussef.
Ana dai bukatar akalla kashi biyu bisa uku mafi rinjaye kafin a cigaba da batun tsigewar.

Ana dai zargin shugabar kasar ta Brazil da badakalar cin hanci da yin almundahana da kudaden gwamnati a yayin yakin neman zabenta shekaru biyu da suka gabata.

Yayinda Uwargida Rousseff ta ci gaba da musanta haka a tsawon lokacin da yan adawa suka kwashe suna kiran a tsigeta .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.