Isa ga babban shafi
Brazil

Shirin Tsige Shugaban Kasar Brazil ya Kankama

Bisa dukkan alamu rikicin siyasar kasar Brazil na iya tafiya da Shugaban kasar Dilma Rouseff, inda ake ganin babu makawa mataimakin shugaban kasar Michel Temer  zai hau kujeran shugabancin.  

Shugaban Brazil Dilma Roussef  tare da mataimakin ta Michel Temer.
Shugaban Brazil Dilma Roussef tare da mataimakin ta Michel Temer. REUTERS/Adriano Machado
Talla

Tun  Talata ne dai Babban jamiyyar dake cikin kawance da Jamiyyar dake mulki a kasar  Brazil ta sanar da ficewa daga kawancen, al’amarin da ke nunawa karara cewa babu makawa Gwamnatin Shugaba Uwargida Dilma Rouseff na gab da kawo karshe.

Jamiyyar ta Brazil Democratic Movement Party, PMDB, a takaice, nan da nan ta umarci Ministocin ta shida dake Gwamnati, da sauran masu rike da mukamai da sunan kawance, dasu tattauara nasu-inasu su fice.

Karkashin tsarin shugabancin Brazil, Shugaban kasar za ta ci gaba da mulkin , amma kuma ficewar wakilan jamiyyun da ake Gwamnatin hadakan da su, zai kara dama mata lissafi a kokarin ganin ba’a tsige ta ba, saboda zargin cin hanci da rashawa.

Mataimakin nata Michel Temer, wanda shine shugaban jamiyyar adawa dake cikin gwamnatin hadin kai,shi ne ake ganin zai haye kujeran mulki.

‘Yan adawa kasar na nacewa domin a tsige ta ne saboda wai ta karya dokokin kasafin kudi na kasar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.