Lula ya zama babban hafsa a Brazil
Shugabar Brazil Dilma Rousseff ta nada tsohon shugaban kasar Inacio Lula da Silva a matsayin babban hafsa a fadar shugaban kasar.
Wallafawa ranar:
Nadin na sa zai ba shi kariya daga tuhumar da ake masa na halarta kudaden haramun, matakin da ake ganin na iya kifar da gwamnatin Rousseff wadda ita ma ke fuskantar irin wannan tuhuma tare da manyan jami’an gwamnatinta.
Al’ummar kasar na ganin Lula da matukar kima, kuma ana ganin wannan nadin zai kara tagomashin gwamnatin Rousseff wanda al’ummar kasar ke neman ganin ta sauka daga mukaminta.
Lokacin mulkin Lula, Rousseff ta rike mukamin babban hafsa a fadar shugaban kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu