Brazil
Shugaban Brazil Dilma Rousseff Na Zargin Mataimakin ta Da yi Mata Zagon Kasa
Shugaban kasar Brazil Uwargida Dilma Rousseff ta zargi mataimakin ta da kulla makarkashiyar tsige ta daga mulki.
Wallafawa ranar:
Talla
Dilma Rousseff ta fadi cikin wani jawabi da ta gabatar cewa ta gano a zahiri cewa mataimakin ta Michel Temer na da hannu wajen kulle-kullen kawar da ita daga madafun iko.
Wakilan majalisar kasar za su fara daukan matakan tsige ta a zaman da za su yi ranar Juma'a mai zuwa.
Farin jinin shugaban ya ragu ainun kasancewa tattalin arzikin kasar ya sukurkuce sosai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu