Isa ga babban shafi
Brazil

Wani ministan Brazil ya sake yin murabus

A Karo na uku, daya daga cikin ministocin sabuwar gwamnatin Brazil ya sauka daga kujerarsa saboda zargin da ake yi masa na karbar cin hanci. 

Shugaban rikon kwarya Michel Temer na daga cikin wadanda ake zargi da tambayar na goro daga hannun tsohon shugaban kamfanin mai na Petrobras, Sergio Machado
Shugaban rikon kwarya Michel Temer na daga cikin wadanda ake zargi da tambayar na goro daga hannun tsohon shugaban kamfanin mai na Petrobras, Sergio Machado Lula Marques/ Agência PT
Talla

Ministan yawon bude ido Henrique Eduardo Alves ya bayyana ajiye mukaminsa bayan wata shaida ta tabbatar da ba shi Dala 445,000 da aka karkata akalarsu daga kamfanin man kasar na Petrobras.

Alves wanda daya ne daga cikin 'ya'yan jam’iyyar PMDB ta shugaban riko Michel Temer  ya ce, ya sauka daga kujerarsa ne don kaucewa shafa wa gwamnatin kashin kaji.

Shi ne dai minista na uku da badakalar cin hanci ta raba da mukamansu bayan ministan tsare-tsare, Romeo Juca da Fabiano Silveira, ministan yaki da cin hanci.

Shugaban kasar na riko Temer da Alves na daga cikin manyan 'yan siyasa 20 da tsohon shugaban kamfanin man Petrobras Sergio Machado ya bayyana a matsayin wadanda suka tambaye shi da ya ba su na goro daga Dala biliyan biyu na kudin man da aka karkata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.