Isa ga babban shafi
Brazil

Majalisar dattawan Brazil za ta tsige Rousseff

Majalisar dattawan Brazil ta lashi takobin kada kuri’ar tsige shugaba Dilma Rousseff duk da cewa majalisar wakilai ta soke kuri’arta wadda ta kada a ranar 17 ga watan Aprilun da ya gabata.

Shugaba Dilma Rousseff ta kasar Brazil
Shugaba Dilma Rousseff ta kasar Brazil REUTERS/Adriano Machado
Talla

Kakakin majalisar dattawan Renan Calheiros ya yi watsi da matakin da mukaddashin kakakin majalisar wakilai, Waldir Maranhao ya dauka na dakatar da shirin tsige shugaba Rousseff wadda ake zargi da cin hanci da rashawa.

Mr. Maranhao ya bukaci a sake kada wata kuri’ar a majalisar wakilan, abinda takwaransa na majalisar dattijai ya ce, ya saba ka'ida.

A ranar Laraba ne majalisar dattijan za ta kada kuri’a a kan yiwuwar fara yunkurin tsige Uwargida Rousseff wadda ake zargi da karya dokokin amfani da kudaden gwamnati.

Matukar dai ta gaza tsallake shirin tsigewar, shugaba Dilma Rousseff za ta fuskanci dakatarwa daga mukaminta tare da fuskantar shari’ar da za a shafe tsawon watanni shida ana gudanarwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.