An tsige Shugaban Majalisar wakilan Brazil
Kotun Kolin Brazil ta dakatar da shugaban Majalisar wakilan kasar Eduardo Cunha, wanda shine na gaba gaba wajen ganin an tsige shugabar kasar Uwargida Dilma Rousseff da ake zargi da karkata makudan kudade.
Wallafawa ranar:
Kotu ta same shi da laifin kokarin hana gudanar da bincike akan sa saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa.
Duk da yake dakatar da shi daga aiki ba zai iya hana yunkurin tsige shugabar ba, amma matakin ya dada fito da yadda matsalar cin hanci da rashawa tayi katutu a yan siyasar kasar Brazil.
Shugabar kasar Uwargida Dilma Rousseff na kokarin gani ta rike kujerar shugabancin kasar inda rahotanni suka tabbatar da cewa ta na kokarin gani ta shawo kan da dama daga cikin yan siyasa don gani an yi watsi da batun tsige ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu