Isa ga babban shafi
Brazil

Majalisar Brazil ta amince da tsige Rousseff

Majalisar wakilan Brazil ta amince da shirin tsige shugabar kasar Uwargida Dilma Rousseff wadda ake zargi da cin hanci da rashawa da kuma halarta kudaden haramun.

Shugaba Dilma Rousseff ta kasar Brazil
Shugaba Dilma Rousseff ta kasar Brazil REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Masu bukatar ganin an tsige shugabar sun samu kuri’u 342 daga cikin 'yan majalisu 513 abinda ya basu damar ci gaba da yunkurin tsige Rousseff.

Yanzu haka dai za su mika rahotan matsayarsu ga majalisar dattawa wadda ita ma za ta dauki matsaya akai.

Rousseff ta yi watsi da zargin da ake ma ta inda ta bayyana yunkurin a matsayin juyin mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.