Isa ga babban shafi
Belgium

An Sake Bude Filin Jiragen Sama na Brussels

An sake bude Filin sauka da tashin jiragen sama na Brussels dake kasar Belgium a yau lahadi bayan an rufe shi tun ranar 22 ga watan jiya a lokacin da aka kai kazamin harin kunar bakin wake da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 32.

Filin jiragen sama na Belgium
Filin jiragen sama na Belgium rfi
Talla

Mutane biyu ne dai aka gano suka kai harin kunar bakin waken wanda kungiyar IS ta masu jihadi ta ce ita ta kitsa.

Tun a jiya shugaban filin jiragen saman Arnaud Feist ya sanar cewa yau lahadi ne za’a dan fara amfani da filin, inda jiragen saman  uku  za su tashi.

An dai dauki tsauraran matakan tsaro, kuma an umarci fasinjoji dasu kasance suna filin jiragen saman sao'i uku kafin jirginsu ya tashi.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.