Harin Brussels: An saki mutum guda
Hukumomi a kasar Belgium sun saki wani mai suna Faycal Cheffou, daya daga cikin mutane uku da ake zargi suna da hannu a mummunan harin da aka kai a Brusssels. An saki mutumin ne saboda babu hujjoji da ke tabbatar da yana da alaka da harin.
Wallafawa ranar:
Jami’an taron Belguim sun koma aikin farautar mutum na uku da a harin bama baman da aka kai a filin tashi da saukar jiragen sama a makon jiya.
Ofishin mai shigar da kara na kasar ya ce bayanan da aka yi amfani da su domin cafke Faycal, ba su gamsar da masu bincike a game da wannan hari ba, saboda haka aka yanke shawarar sakin shi.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘yan sanda ke fitar da sabon hoton mutum na 3 da ake zargi da harin na 22 ga watan Maris a fillin jirgin Zaventem
Sabbin alkalumar mamamatan da aka fitar sakamakon harin sun kai 35 a yanzu, bayan 4 daga cikin wadanda ke jinya a asibiti sun kwanta dama.
Yanzu dai an tabbatar da cewa Faycal Cheffou da ya bayyana kansa a matsayin dan jarida mai zaman kansa ba ya cikin maharan Brussels.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu