Isa ga babban shafi
Belgium

Belgium ta cafke mutane 6 saboda harin Brussels

Hukumomi a kasar Belgium sun ce kawo yanzu an cafke mutane 6 wadanda ake zargi da hannu wajen kai wa kasar hare-hare a ranar Talatar da ta gabata har aka samu hasarar rayukan mutane 31.

Harin Brussels ya kashe mutane fiye da 30
Harin Brussels ya kashe mutane fiye da 30 路透社照片
Talla

Wani lokaci a yau sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai isa birnin Brussels, domin nuna jajen Amurka a game da wadannan hare-hare da aka kai birnin wanda shi ne cibiyar kungiyar tarayyar Turai da kuma kungiyar tsaro ta Nato.

Hukumomi sun ce, filin jiragen saman Brussels zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

Tuni dai kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaddamar da harin wanda ya auku bayan kama Salah Abdeslam, babban wanda ake zargi da kitsa harin birnin Paris na kasar Faransa a watan Nuwamban bara, abinda ya yi sanadin mutuwar mutane 130.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.