Isa ga babban shafi
Belgium

Hukumomin Belgium sun tantance maharanta

Hukumomi a kasar Belgium sun ce, an tantance 3 daga cikin mutane 4 da suka kai hari a filin sauka da tashin jiragen sama da kuma tashar jirgin kasa da ke birnin Brussels a ranar Talatar da ta gabata, hare-haren da su ka yi sanadiyyar mutuwar mutane 31.

Harin Brussels ya kashe mutane fiye da 30
Harin Brussels ya kashe mutane fiye da 30 REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Mai shigar da kara na gwamnatin kasar ya ce Ibrahim da kuma Khalid El Bakraoui wadanda ‘yan uwan juna ne, su suka kai hari a filin jiragen saman Zaventem da tashar jiragen kasa ta Maalbeek, yayin da aka bayyana Najim Laacharaoui a matsayin mutum na uku da ya kai harin na filin jiragen saman.

Wani lokaci a yau ne dai ministocin cikin gida na shara’a daga kasashen Turai za su yi taro domin duba halin da yankin ke ciki bayan harin na Brusssels.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na kan hanyarsa ta zuwa Brussels don mika jajen Amurka dama goyon bayan da za su bayar a kokarin lalubo masu hannu a mummunan harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.