Isa ga babban shafi
Belgium

An gano wadanda suka kai hari birnin Brussels

An gano 'yan kunar bakin wake uku da suka kai hari, a babban filin jirgin saman Zaventum da ke birnin Brussels na Belgium.

Maharan Fillin jirgin Zaventem dake Birnin Brussels
Maharan Fillin jirgin Zaventem dake Birnin Brussels AFP PHOTO / BELGIAN FEDERAL POLICE
Talla

Kafar watsa labaran Belgium ta ambato sunayen wadanda ta ce 'yan uwan juna ne wato Khalid da Ibrahim el-Bakraoui kuma sanannu ne ga 'yan sanda da aka gano kawo yanzu.

Shugabanni Kasashen duniya sun hada kan su wajen Allah wadai da kazamin harin da aka kai birnin Brussels wanda ya hallaka mutane 36, inda su kayi alkawarin murkushe kungiyar ISIS da ta dauki alhakin kai harin.

Kungiyar kasashen Turai ta bayyana harin a matsayin wanda aka kaiwa demokradiyar da ta sha alwashin karewa.

Shugaban Amurka Barack Obama da Francois Hollande na Faransa, da Vladimir na Putin da Muhamamdu Buhari na Najeriya da kuma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya duk sun yi Allah wadai da harin.

Harin Jiya talata ba karamin Razani ya jefa a Turai ba, wanda ke zuwa kwananki kalilan bayan Cafke Salah Abdeslam maharin birnin Paris.

Belgium dai ta ayyana makokin kwanaki uku domin alhinin abin da ya faru.

Kungiyar IS take sake zama babban barazana a duniya, tace babu shaka ita ta kai wannan hari daya salwantar da rayuka sama da 30, yayin da wasu sama da 100 ke kwance a Asibiti cikin rauni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.