Isa ga babban shafi
Faransa-Belgium

Lauyan Salah Abdeslam zai kalubalanci Faransa

Wani fitaccen lauyan kare wadanda ake tuhuma da ta’addanci dan kasar Belgium, ya sha alwashin tsayawa Salah Abdeslam wanda ake zargi da kitsa kai harin birnin Paris a bara.

Lauya Salah Abdeslam, Sven Mary a Brussels
Lauya Salah Abdeslam, Sven Mary a Brussels REUTERS/Eric Vidal
Talla

Lauyan mai suna Sven Mary ya yi fice wajen kare mutanen da ake tuhuma da laifukan ta’addanci, kuma yace zai tsayawa matashi Salah Abdeslam tare da kalubalantar babban mai shigar da karar Faransa Fransuwa Molins kan abunda ya kira boye gaskiya abinciken da ake yiwa Saleh.

Faransa dai ta jima tana neman Salah ruwa ajallo tun bayan da aka gano shine ka dai ya tsira daga cikin maharan birnin Paris da suka hallaka mutane 130.

Bayan wata ganawa da wanda yake karewar a shelkwatar ‘yan sandan kasar Belgium lauya Sven ya ce zai yaki bukatar faransa na mika mata matashin ta hukunta shi abun da lauyan ke gani za a take hakkin saleh.

A cewar Sven baiga dalilin da za a yi amfani da jefa razani a zukatan jama’a da nufin neman suna ba.

A baya dai wannan lauya ya taba tsaya wa fitaccen madugun ‘yan jihadin nan mai suna Fu'ad Belkassim daya horas da matasan Belgium da dama da a yanzu haka suka zama mayakan kungiyar IS.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.