Isa ga babban shafi
Belgium

An samu tutar ISIS a samamen Brussels

'Yan sanda a kasar Belguim sun ce, sun samu tutar kungiyar mayakan ISIS tare da dan kasar Algerian nan da aka kashe lokacin da suka kai samame a wani gida da ke birnin Brussels, kuma yanzu haka suna neman wasu mutane biyu ruwa a jallo.

'Yan sanda sun kai samame a Brussels saboda harin birnin Paris da ya kashe mutane 130.
'Yan sanda sun kai samame a Brussels saboda harin birnin Paris da ya kashe mutane 130.
Talla

An dai bayyana wanda aka kashe a matsayin Mohammed Belkaid, dan asalin kasar Algeria da ke zama a Belguim ba bisa ka'ida ba.

Firaministan Belguim Charles Michel ya ce, da yiwuwar a kai wa kasar harin ta’addanci lura da rawar da jami'anta suka taka wajen kashe Belkaid mai shekaru 35, lamarin da yasa hukumomin kasar suka kara kaimi wajen tabbatar da tsaro.

A ranar Talata ne rundunar 'yan sanda da ta kunshi jami'an Belgium da Faransa suka kaddamar da samame  a Brussels, a wani mataki mai nasaba da harin ta'addancin da kungiyar ISIS da kai birnin Paris a watan Nuwamban bara, inda ta kashe mutane 130.
 

A banagae guda, hukumomin Faransa sun ce, sun kama wasu mutane guda hudu da ake zargin mayakan jihadi ne yayin da shugaban kasar Francois Hollande ya gargadi al'ummar kasar da su kula sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.