Isa ga babban shafi
Belgium

An gano gidaje uku da aka yi anfani dasu a kitsa harin Paris

‘Yan sanda a Belgium sun ce sun gano wasu gidaje uku wadanda maharan nan da suka kai hari Paris suka rika yin amfani da su domin tsara yadda za su kai hare-haren na watan nuwambar bara inda aka samu asarar rayukan mutane 130.

Yan sandan kasar Belgium
Yan sandan kasar Belgium REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Eric Van Der, mai magana da yawun ma’aikatar shari’ar kasar Belgium ya ce ana ci gaba da bincike kan wannan lamari da ya yi matukar girgiza kasashen Turai.

Tun bayan kai jerin hare haren ne kasashen Nahiyar Turai suka bazama neman sauran maharan da suka tsere daga Birnin na Paris, inda kasar Belgium ta yi ta kamen wadanda ake zargi da hannu a harin.

Mutane sama da 100 ne suka rasa rayukansu a harin na Paris a yini guda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.