Gwamnatin Belgium ta soke wasan wuta na shekara
Kasar Belguim ta soke bikin wasan wuta da aka saba yi don maraba da sabuwar shekarar 2016 saboda barazanar kai harin ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Hukumomin kasar sun ce an soke bikin da ya tara mutane sama da 100,000 bara saboda kare lafiyarsu, kuma matakin na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun yi wa wasu mutane biyu tambayoyi kan alakarsu da wadanda suka kai hari birnin Paris na Faransa, inda sama da mutane 100 suka rasa rayukansu.
Hukumomin Faransa suma sun soke bikin da aka saba yi a birnin Paris, kuma an girke jami'an 'yan sanda da sojoji 11,000 domin tababtar da tsaro.
Kasashen Turai da dama sun dauki matakan tsaro saboda abinda suka kira barazanar kai hari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu