Isa ga babban shafi
Faransa-Belgium

‘Yan bindiga sunyi ruwan arsashai kan ‘yan sanda Faransa da Belgium

Gwamnatin Faransa ta ce, ‘yan bindiga sun yi ruwan arsashai kan jami’an ‘yan sandanta da na kasar Belgium bayan sun kai samame a Brussels sakamakon harin birnin Paris wanda ya hallaka mutane 130 a bara.

'Yan sanda a Faransa
'Yan sanda a Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar jaje a kasar Ivory Coast bayan harin ta’addancin da wata kungiya mai alaka da al’Qaeda ta kaddamar kan wani Otel da ke gabar teku, abinda ya yi sanadin mutuwar mutane 18 cikin su kuwa har da Faransawa hudu.

Mr. Cazeneuve ya ce, an yi amfani da makamai wajen kaddamar da farmaki kan rundunar ‘yan sandan wadda ta kunshi jami’an Faransa da Belgium bayan ta kai samame a Brussels, a wani mataki na kokarin kame wadanda ake zargi da hannu a hare a haren da kungiyar ISIS ta kai birnin Paris a bara tare da kashe mutane kimanin 130.

Mr. Cazeneuve ya kara da cewa, dole ya yi taka-tsan tsan a kalamansa, lura da cewa a halin yanzu rundunar ‘yan sandan na kan aikin samemen, kuma ya ce, ba zai yi tsokaci fiye da abinda ya sanar ba.

To sai dai wasu rahotanninn sun ce, ‘yan bindigan sun jikkata ‘yan sanda uku bayan sun bude musu wuta a samamen na Brussels, kuma daya daga cikinsu na cikin mummuan hali saboda harsashin da ya same shi a cikin kunnensa da kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.