Harin Paris: Faransa da Belgium sun fadada samame
‘Yan sanda a Faransa sun kai sabbin samame a wurare 128 da ake zaton maboyan ‘yan ta’adda ne a cikin kasar, tare da sanya Jami’an tsaron dubu 115 cikin shirin ko-ta kwana bayan harin ta’addanci da ya kashe mutane 132 a birnin Paris.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumomin Faransa da ma na Belgium sun tsaurara samame a yankunan daban-daban na kasashen su domin gano ‘yan ta’adda da ke boye a kasashen.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ke ziyara a faransa yanzu haka, ya baiyana maharan a matsayin ba ta gari tare da allawadai da lamarin
Kerry ya kuma bayyana cewa Wannan yaki ne ba wai kawai na Faransa ba, yaki ne a kan daukacin al'ummar duniya"
A halin da ake ciki dai yanzu haka ‘Yan sanda Faransa na neman Salah Abdeslam mai shekaru 26, kuma daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a kai hare-haren bayan anyi amannar cewa ya tsere ta kan iyakar kasar zuwa kasarsa, Belgium.
A cewar Ministan cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve, har yanzu sun gagara tan-tance mutane nawa ne ke da hannu a hari, sai dai sun yi wa mutane 100 yanzu haka daurin talala wasu 23 kuma na hannu hukuma.
Ita ma Jamus da ke taimakawa Faransa farauta masu hannu a harin kasar, a yanzu sun cafke wani mutumi guda da mata 2 a kusa da iyakar Belgium sai dai kawo yanzu ba ta tantace ko suma ‘yan ta’adda ba ne
Kazalika Britaniya ta sanar da cafke wasu maza 2 a kasarta masu shekaru 22 da 20, wanda suke tunani na da alaka da harin na birnin Paris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu