Isa ga babban shafi
Belgium

Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga a kasar Belgium

‘Yan sandan kasar Belgium sun cafke mutane 13 tare da bindige wasu mutane biyu da ake zargin cewa masu tsatsauran ra’ayin kishin addini ne wadanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar. Wannan kuma na ci gaba da haifar da fargabar barazanar hare hare a kasashen Turai bayan harin Paris.

'Yan sandan Belgium Verviers
'Yan sandan Belgium Verviers REUTERS/Stringer
Talla

‘Yan sandan sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda a wata musayar wuta da suka yi a garin Verviers sakamakon wasu bayanan sirri da aka samu a da ke tabbatar da cewa ‘yan bindigar na shirin kai hari.

Ministan harkokin wajen kasar ta Belgium Didier Reynders ya ce samamen da aka kai domin murkushe wadannan mahara, alama ce da ke tabbatar da cewa jami’an tsaro na cikin shiri domin kare kasar daga ‘yan ta’adda.

Yanzu haka dai an tsauraran matakan tsaro a sauran sassan kasar lura da halin da ake ciki a Turai, bayan harin da aka kai wa Faransa a cikin makon jiya.

Irin wannan samamen ne aka kaddamar a Faransa da Jamus inda aka cafke mutane da dama da ake zargin suna kulle kulle kai hari.

Masana na ganin kasashen yammacin Turai za su fuskanci barazanar hare hare bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a Faransa

A baya can wani da ake zargin ya fito yaki daga Syria, ya taba kai hari a kasar birnin Brussels inda ya kashe mutane 4.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.