Isa ga babban shafi
Faransa

Harin Paris: An gabatar da tuhuma kan Salah Abdelsalam

An gabatar da tuhuma a hukumance kan Salah Abdelsalam babban mutumin da ake zargi da kai harin Paris a bara. Sai dai Lauyansa ya ce zai kalubalanci yunkurin tasa keyarsa daga Belgium zuwa Faransa.

Maharin Birnin Paris Salah Abdelsalam
Maharin Birnin Paris Salah Abdelsalam REUTERS
Talla

Lauyan yace Salah Abdelsalam wanda aka kama yayin farmaki a Brussels ranar Juma'a yana bada hadin kai ga hukumomin Belgium.

Kasar Faransa ta ce kame Salah Abdelsalam babban koma baya ne ga Kungiyar IS dake barazanar tsaro a kasashen Turai.

A cewar ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve samame da aka kai ‘yan kwanankin nan ancafke mutane da dama wadanda kasantuwar cikin Turai babban illar ce, kuma wannan ya nuna cewa tabbas zasu yi Nasara a yakin da sukeyi da ta‘addanci.

Hukumomin tsaro dai na fatan Saleh zai bada cikakken bayani game da kungiyar ta masu ikrarin jihadi.

Sale Abdesalam da aka jimma ana neman sa ruwa a jallo, anyi nasaran cafke shi a lokacin wani samame a yankin Molenbeek da ke Brussels, kuma an harbe shi a kafa.

Mutane 130 suka mutu a harin na Paris a watan Nuwamba.

Yan sandan kasa da kasa sun bukaci ayi taka tsantsan a kan tsaron iyakokin kasa da kasa domin dakile yunkurin tserewar abokan hadin kan Abdelsalam daga cikin turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.