Isa ga babban shafi
Faransa-Belgium

An kama Salah Abdesalam daya daga cikin maharan Paris

Gwamantin Belgium ta bakin Theo Francken, wani jami’in ‘yan sanda kasar ne ya sanar da nasarar cafke Salah Abdelsalam da aka dadde ana nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a hare-haren birnin Paris

Salah Abdeslam, daya daga cikin maharan da ake zargi da kai hari a birnin Paris
Salah Abdeslam, daya daga cikin maharan da ake zargi da kai hari a birnin Paris Reuters
Talla

Salah Abdelsalam na daga cikin wadanda ake zargi da kai hare-hare a wurare daban daban  a birnin Paris na kasar Faransa a Nuwambar bara inda mutane sama da 130 suka rasa rayukansu, baya ga wasu da dama da suka jikatta sakamakon jerin hare-haren

Tun bayan aukuwar munmunar harin da ya matukar girgiza al’ummar kasar aka yi ta neman Salah a ciki da wajen Faransa ba tare da yin nasara ba, kasashen Turai da dama sun shiga cikin aikin bincike don gano inda yake ba a kuma samu biyan bukata ba kafin daga bisani yau juma'a kasar Belgium ta fitar da sanarwar kama dan ta’addan dake da alaka da kungiyar ISIL mai da’awar jihadi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.