Isa ga babban shafi
Belgium

Belgium ta yi karin haske kan maharanta

Hukumomin kasar Belgium sun yi karin haske game da mutane biyu da suka kai kazamin harin ta'addanci a filin jiragen sama da ke Brussels, yayin da aka ci gaba da gudanar da bincike.

Hukumomin Belgium na cin gaba da bincike sakamakon harin da aka kaddamar a filin jirgin sama da tashar jirgin kasa na kasar, abinda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 40
Hukumomin Belgium na cin gaba da bincike sakamakon harin da aka kaddamar a filin jirgin sama da tashar jirgin kasa na kasar, abinda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 40 REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Frederic Van Leeuw, babban mai gabatar da kara na Belgium ya yi wa manema labarai bayani cewa ‘yan kunar bakin waken biyu ne, Ibrahim El Bakraoui da  dan uwansa Khalid wanda ya makale a tashar jirgin kasa a lokacin da bam din ya tarwatse ya kashe mutane 31 da jikkata wasu mutune 270.

A cewar mai gabatar da karan, mutun na uku ya tsere ne kafin tarwatsewar bama-baman da kungiyar IS mai ikirarin jihadi ta amsa cewa ita ta kitsa.

Mai gabatar da karan na cewa akwai sinkin wani shirgegen bam da bai tashi ba, da mutun na uku ya bari a cikin kayan da ya ke turawa a filin jirgin sama na Zaventum.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta Belgium ta ce tana sane da Khalid da kuma Ibrahim El Bakraoui, wadanda duk ‘yan asalin Belgium ne, kuma an sansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan suna da alaka da kai harin ta'addanci na Paris a watan 11 na shekarar da ta gabata.

Mamata sakamakon harin na jiya, kamar yadda hukumomin kasar su ka yi bayani sun kunshi ‘yan kasashen Birtaniyya da Columbia da Equador da Faransa da Portugal da Amurka.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.