Belgium
An soke taron gangamin adawa da ta'addanci a Brussels
Hukumomin kasar Beligium sun bukaci al’ummar kasar da su kaurace wa halartar taron gangami da aka tsara gudanarwa a gobe lahadi domin yin tir da ayyukan ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Talla
Magajin garin birnin Brussels Yvan Mayeur, ya ce har yanzu akwai barzanar sake kai hare-hare a birnin, saboda haka bai kamata jama’a su halarci duk wani taro na gangami ba sai a cikin makonni masu zuwa.
Ministan cikin gidan kasar Jan Jambon ya goyi bayan wannan mataki da magajin garin Brussels ya dauka. Tuni dai wadanda suka shirya zanga-zangar suka amincewa da wannan mataki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu