Isa ga babban shafi
Faransa-Belgium

Ana farautar wadanda ake zargi da kai haren-haren Brussels

Hukumomin kasar Belgium sun ce a jimilce an cafke mutane hudu a halin yanzu wadanda ake zargi da hannu wajen kai hari a filin sauka da tashin jiragen saman Brussels, da kuma wani harin a tashar jirgin kasa da karkashin kasa a makon da ya gabata. 

'Yan sanda a kofar tashar jirgin kasa a birnin Brussels, Belgium,22 ga watan maris, 2016.
'Yan sanda a kofar tashar jirgin kasa a birnin Brussels, Belgium,22 ga watan maris, 2016. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Hakazalika ofishin mai shigar da kara na kasar ya ce jami’an tsaro sun kai samame a wurare daban daban har 13, daya birnin Malines da kuma wani daya a birnin Duffel a yankin da ke amfani da harshen Flamande na arewacin kasar, yayin da aka kai sauran samamen a birin Brussels.

 

Hukumomin tsaro na kasashen Yankin Turai sun ce suna neman mutane 8 da suke zargi da hannu wajen kai hare-hare a biranen Paris da kuma Brussels.

Mutanen da ake nema, dukkaninsu na da alaka da AbdelHamid Abaoud, wanda aka bayyana shi a matsayin jagora wajen kitsa kai harin birnin Paris, amma an kashe shit un ranar 18 ga watan nuwambar bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.