Isa ga babban shafi
Belgium

'Yan sanda sun tarwatsa masu bore a Brussels

‘Yan sandan Belgium sun yi amfani da ruwan zafi da kuma hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa wata zanga-zanga da masu zazzafar kishin kasa suka gudanar a birnin Brussels domin nuna bacin ransu a game da harin ta’addancin da aka kai wa kasar a makon jiya.

Jami'an tsaron Belgium sun tarwatsa taron masu zanga zangar ta hanyar jefa masu hayaki mai sa kwalla.
Jami'an tsaron Belgium sun tarwatsa taron masu zanga zangar ta hanyar jefa masu hayaki mai sa kwalla. REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Wasu matasa ne da aka ce yawansu ya haura dari biyu, suka yi wannan zanga-zanga a daidai lokacin da jama’a ke juyayi don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta’addanci da aka kai birnin na Brussels da kuma Paris da ke makociyar kasar wato Faransa.

Tarzomar ta kazance ne a lokacin da matasan suka fara jifar ‘yan sanda da duwatsu yayin da wasu ke cinna wuta a kwalaben da aka makare su da man fetur domin jefa wa ‘yan sanda, to sai dai majiyoyin tsaro sun ce, an cafke akalla 10 a wannan zanga-zangar.

Kafin nan dai mai shigar da kara na gwamnatin tarayyar Belgium, ya ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a hare-haren da aka kai wa kasar a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce, an kai samame har sau 13 a wurare daban daban kuma an cafke mutane 4 da ake zargi.

A can kuwa kasar Italiya, jami’an tsaro sun sanar da kama wani dan kasar Algeria da ake zargi da hannu a batun na Belgium, to sai dai majiyoyi sun ce, wanda ake zargin mai suna Djamalud Dine Ouali mai shekaru 40, ya ki cewa jami’an tsaro uffan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.