Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta sake chilla shu'umin makami

Kasar Koriya ta Kudu ta yi zargin cewa, makwabciyarta Korea ta Arewa ta sake chilla wani shu'umin makamai mai linzami a yau Juma'a kuma a daidai wani lokaci da wasu shugabannin kasashen duniya ke duba batun makamai na nukiliya a wani taro da su ke yi a birnin Washington na kasar Amurka.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na kallon yadda jami'ansa ke haarba makami mai linzami
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na kallon yadda jami'ansa ke haarba makami mai linzami REUTERS/KCNA/Files
Talla

Ma'aikatan gabar ruwa na Koriya ta Kudu sun ce, ko shakka babu an chilla makamin, kuma har wasu kananan jiragen kamun kifi guda 70 sun kasa zuwa sana'arsu.

Harin na yau na zuwa ne a wani lokaci da shugaban Amurka Barack Obama ke karban bakwancin wasu shugabannin kasashen duniya da ke muhawara na kwanaki biyu game da illar makaman nukiliya, inda mahalartarsa ke tabo batun gwaje-gwajen da Koriya ta Arewa ke yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.