Isa ga babban shafi
Korea ta arewa

Koriya ta sake harba makamai duk da takunkuman MDD

Kasar Koriya ta Arewa ta sake harba wasu jerin makamai guda shida a cikin teku a yau Alhamis duk da  takunkuman karya tattalin arziki masu zafi da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kakaba mata a jiya Laraba sakamakon gwajin makamin Nukiliya da kuma harba Roka.

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong
Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong 路透社
Talla

Kakakba takunkuman na zuwa, bayan kwamitin mai wakilai 15 ya amince da kudirin da Amurka ta gabatar bayan cimma yarjejeniya tsakaninta da China, wadda kawa ce ga kasar ta Koriya ta Arewa.

Bayan wani zama da kwamitin ya yi kan batun karya dokokin da Koriya ta Arewa ta yi ne, kafatanin mambobin kwamitin suka amince da bukatar kakaba takunkuman.

Shugaba Barrack Obama na Amurka ya yi na'am da matakin yana mai cewa hakan shi ne dai dai bisa kunnen kashin da Koriya ta Arewan ta yi na gwajin makamin Roka da kuma Nukiliya.

Daga cikin takunkuman dai har da na katse zirga zirgar jiragen sama da kuma daina cinikin makami da ita da kuma binciken kwakwaf kan jiragen kaya da ke tasowa daga kasar ko kuma zuwa kasar da kuma daina cinikin kayayyakin alatu da Koriyan sai kuma sallamar jami’an diplomasiyarta daga kasashe mambobin Majalisar dinkin duniya

Akwai kuma takunkumin dakatar da cinikaiyyar ma’adinai, kazalika bangaren bankuna na cikin matsi don kuwa za a rufe dukkanin wasu harkokin hada hadar kudade na kasar da ke kasashen waje.

Amma duk da jerin takunkuman, Koriya ta Arewa bata razana ba yayin da ta sake gwajin wasu makaman a yau din nan, matakin da ke nuna cewa ko a jikinta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.