Isa ga babban shafi
MDD-Korea ta Arewa

Ban Ki-Moon ya bukaci korea ta Arewa ta Jingine gwajin makamin Roko

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci kasar Korea ta Arewa ta jingine shirnta na gwajin wani mugun makamin roka da za ta yi wanda ya ce ya sabawa dokokin duniya na fasahar kera makamai.

Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon
Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon 路透社照片
Talla

Banki Moon ya ce abu ne mai matukar muhimmaci kasar Korea ta Arewa ta dakatar da shirin gwajin makamain da zata yi a ranar Litinin mai zuwa domin matakin ya keta dokokin fasaha na duniya.

Kiran na Ban Ki moon na zuwa ne bayan kasar ta sanarwa hukumomin MDD cewa zata yi gwajin makamin Roka duka makwanni uku bayan ta gwada wani mugun makami nukiliya a karo na hudu.

Tuni dai Amurka da Korea ta kudu dake takun saka da korea ta arewa suka gargadi kasar kan shirin gwajin makamin.

A nata bangaren kuma China ta bayyana damuwar ta ne ga shirin na koriya da suke amintaka da juna.

Ban ki moon dai wanda dan kasar Korea ta kudu ne yana ta kokarin bin hanyoyin lalama wajen ganin Korea ta Arewa ta bi umurnin MDD domin rage barazana a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.