Isa ga babban shafi
MDD-CHINA-JAPAN

MDD ta yi watsi da korafin Japan kan ziyarar Ban zuwa China

Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da korafin da kasar Japan ta yi kan ziyarar Sakatare Janar na Majalisar Ban Ki Moon zuwa China dan halartar faretin soji a Beijing dan tunawa da nasarar da aka samu a yakin duniya na biyu.

Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon.
Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ita dai Japan ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta tsaya a matsayin yar ba ruwan mu ne kan bikin nasarar da aka samu shekaru 70 da suka wuce, amma sai kakakin Sakataren Stephane Dujarric y ace Ban ya halarci irin wannan taruruka a kasashe da dama.

Ana saran China za ta yi anfani da bikin wajen nuna sabbin makaman ta na yaki da kuma faretin sojoji dubu 12.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.