Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Koriya ta kudu da Japan sun gargadi Koriya ta arewa

Kasashen Koriya ta kudu da Japan sun jaddada gargadin da Amurka ta yi na cewa Koriya ta arewa za ta dandana kudanta da zaran ta ci gaba da shirinta na kokarin harba Roka bayan ‘yan makwanni da ta yi gwajin makamin Nukliya.

Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un
Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un © REUTERS/KCNA
Talla

Gwamnatin Koriya ta kudu ta bukaci Koriya ta arewa da ta janye daga shirinta na harba Rokan nan da mako mai zuwa yayin da ta ce, kokarin harbawar wani matakin karya dokar majalisar dinkin duniya ne kuma tsokana ce kai tsaye ga sauran kasaahen duniya.

A na shi bangaren, firaministan Japan Shinzo Abe ya caccaki abinda ya kira takala da kuma karan tsaye ga dokoin kasa da kasa da Koriya ta arewa ke yi.

Gargadin dai na zuwa ne kwana guda da Koriya ta arewa ta ayyana tsakanin ranakun 8 zuwa 25 na watan Fabairu a matsayin lokacin da za ta harba Rokan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.