Isa ga babban shafi
Korea ta arewa

Koriya ta arewa ta kare kanta

Kasar Koriya ta Arewa ta kare gwajin makamin da ta yi, tana mai cewa makomar Saddam Hussain na Iraq da Moammar Ghaddafi na Libya ya tabbbatar da abinda ke faruwa ga kasashen da suka yi watsi da shirinsu na mallakar makaman Nukiliya.

Shugaban Korea ta arewa  Kim Jong Un
Shugaban Korea ta arewa Kim Jong Un REUTERS
Talla

Sannan kasar ta yi gargadi ga makwabciyarta Koriya ta kudu akan ta shiga taitayinta ga Farfagandar da ta soma akan iyakokinsu domin matakin na iya jefa su cikin yaki.

Koriya ta arewa sake fitar da wani hoton bidiyo a yau Asabar wanda ya nuna yadda ta yi nasarar gwajin wani makami mai linzami bayan ta yi gwajin wani babban makamin bom na Hydrogen da ya razana duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.