Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

MDD za ta sanya takunkumi kan Koriya ta Arewa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi barazanar gabatar da sabbin takunkumin hukunta kasar Koriya ta Arewa bayan ta yi gwajin makamin Nukiliyar hydrogen wanda ya janyo mata suka daga sassan duniya.

Shugaban koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban koriya ta Arewa Kim Jong Un REUTERS/Kyodo
Talla

Wannan gwaji na makamin hydrogen da Koriya ta Arewa ta yi ya gamu da suka da kuma Allah-wadai daga sasan duniya ciki har da kawarta wato China wadda ta ce, ba ta goyan bayan matakin.

China tare da kasashe 15 na kwamitin sulhu sun soki matakin inda suka bayyana shirin shata wasu sabbin takunkumai domin hukunta kasar wadda ta fara gwajin makamin atomic a shekarar 2006.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bukaci kasar ta daina daukar matakan takala, bayan sukar da kasashen Koriya ta kudu da Amurka da Faransa suka yi.

Sai dai Amurka ta bayyana shakku dangane da gwajin inda ta ke cewa, inda da gaske ne karar da za a ji, da ya zarce wanda aka ji lokacin gwajin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.