Korea ta Kudu da ta Arewa sun gana akan sabaninsu
Kasashen Korea ta Kudu da Korea ta Arewa sun gudanar da wata tattaunawa da nufin cimma matsaya akan tankiyar da ke tsakaninsu game da kan iyakokinsu, al-amarin da ya kusan haifar da yaki a tsakaninsu.
Wallafawa ranar:
Duk da dai ana fatan duk wata tattaunawa a tsakanin kasashen biyu za ta taka rawar gani, amma lura da zaman da suka gudanar a baya, mawuyaci ne su cimma matsaya mai dorewa.
Kusan shekaru biyu kenan da suka gudanar da irin wannan zaman da nufin zantawa kan jerin batutuwan da suka shafe su, yayin da suka dau shekaru da dama suna takun tsaka da juna.
Shugaban wakilan Korea ta Kudu Hwang Boo-Gi ya fada wa takwaransa na Korea ta Arewa Jon Jong-Su cewa, ya kamata su taka gagarumar rawa wajan samar da hanyoyin inganta hulda a tsakaninsu kuma ya yi fatan za su magance jerin matsalolinsu daya bayan daya.
A ganawarsu ta farko a safiyar yau jumma’ kasashen biyu sun shafe tsawon minti talatin, inda wakilan bangaorin biyu suka bayyana shirinsu na kawo karshen tankiyar amma daga bisani sun sake dawo wa a maraicen yau domin ci gaba zaman, kuma sun dau tsawon lokaci suna ganawa.
Zaman na yau dai na zuwa ne kwana guda da sanawar da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-Um ya fitar, inda ya ce, kasarsa ta kirkiri wani Bam daga makamashin Nukliya, lamarin da jefa shakku a zukatan Amurka da Korea ta Kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu