Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Koriya ta arewa ta sake harba makami mai linzami

Kasar Koriya ta arewa ta sake harba makamai masu linzami kamar yadda hukumomin Amurka da Koriya ta kudu suka tabbatar.

Amurka ta yi Allah wadai da gwajin makamai masu linzami da Koriya ta arewa ta yi
Amurka ta yi Allah wadai da gwajin makamai masu linzami da Koriya ta arewa ta yi 路透社
Talla

Jami’an sojin Koriya ta kudu sun ce, an harba makamin farko ne da misalin karfe 5:55 na safiayar yau jumma’a agogon kasar, kuma sai da makamin ya yi nisan kilomita 800 a sararin samaniya kafin ya tarwatse cikin teku.

Bayan minti 20 da harbin farko, Koriyan ta arewa ta sake harba makami na biyu kuma dukkanin makaman kirar Rodong ne mai matsakaicin zango da kuma ke iya zuwa kasar Japan.

An kiyasta cewa makamin na Rodong na iya tafiyar kilomita 1,300.

Tuni dai Amurka ta bukaci Koriya ta arewa da ta daina tayar da hankulan jama’a a yankin kuma wannan na zuwa ne kwana guda da shugaba Barck Obama ya kakaba ma ta sabbin takunkumai bayan ta yi gwajin makamin nukiliya duk da an haramta ma ta yin haka.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.