Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Hoton bidiyon farfagandar Koriya ya tarwatsa birnin Washington

Hukumomi a Koriya ta Arewa sun fitar da wani hoton bidiyo da ke nuna yadda kasar ta kai wa Amurka hari da makamin nukiliya wanda ya yi kaca-kaca da birnin Washington, kamar dai yadda wannan hoto da ake kallo a matsayin na farfaganda ya nuna.

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un Reuters
Talla

Bidiyon mai tsawon mintuna hudu, ya nuna yadda sojin ruwan kasar ta Koriya suka kai harin da ya lalata Washington tare da nuna tutar Amurka na ci da wuta.

A karshen wannan hoto dai an rubuta wani sako da ke cewa, ‘’ idan salon mulkin mallakar Amurka ya tunkare mu ko da inci daya ne, to za mu kai wa kasar hari da nukilya.’’
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.